Isa ga babban shafi

Benzema ya kawo karshen bugawa Faransa wasanni

Tauraron dan wasan Real Madrid Karim Mostafa Benzema ya sanar da kawo karshen bugawa kasarsa ta Faransa wasa, kwana guda bayan kammala gasar cin kofin duniyar da Argentina ta lashe a kasar Qatar. 

Karim Benzema dan wasan Real Madrid da ke kasar Spain
Karim Benzema dan wasan Real Madrid da ke kasar Spain AFP - FRANCK FIFE
Talla

A sakon da ya aike ta kafar twita, Benzema yace yayi iya bakin kokarinsa domin kawowa matsayin da yake kai ayau, tare da yin kura kurai a wasu lokuta da kuma samun nasarori, kuma yana mai alfahari da yadda rayuwarsa ta kasance. 

Benzema na daga cikin tawagar ‘yan wasan da aka sarai zasu bugawa Faransa wasa a kasar Qatar, amma sai raunin da ya samu lokacin da yake bugawa kungiyarsa wasa ta hana shi. 

‘Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon D’or saboda ficen da yayi a wannan shekara, ya kafa tarihi wajen zirara kwallaye a kungiyarsa ta Real Madrid, abinda ya taimaka mata samun nasarori daban daban. 

An dai haifi Benzema ne a ranar 19 ga watan Disambar shekarar 1987 a birnin Lyon dake kasar Faransa, kuma iyayen sa sun fito ne daga kasar Algeria, yayin da ya fara wasansa a kungiyar Olympique Lyonnais a shekarar 2008, inda ya zama gwarzon ‘dan wasan shekara da kuma zama wanda yafi kowa jefa kwallaye a raga. 

Wannan nasara ta sa kungiyar Real Madrid ta saye shi akan euro miliyan 35, abinda ya haifar da mahawara a ciki da wajen Faransa, musamman ganin ya koma inda zai yi wasa da fitattun ‘yan kwallo irinsu Cristiano Ronaldo da Gareth Bale. 

Barín Ronaldo Madrid ya budewa Benzema kofar jagorancin kungiyar a gaba, inda ya dinga jefa kwallayen da suka taimakawa kungiyar samun nasarori da dama. 

Bayan bugawa Faransa wasanni a matakin ‘yan kasa da shekaru 17 da 18 da 19 da kuma 21, Benzema ya zarce zuwa babar kungiyar inda ya gamu da matsala lokacin da aka zarge shi da kokarin batawa abokan wasansa suna, abinda ya kaiga dakatar da shi na shekaru 5. 

Nasarar da ya samu a Madrid ta sanya mai horar da ‘yan wasan kasar Didier Deschamp sake mayar da shi cikin kungiyar domin ganin ya buga wasannin da aka kammala a Qatar amma sai rauni ya hana shi. 

Benzema ne ‘dan wasan Faransa na 5 da ya lashe kyautar Ballo D’or ta zaratán ‘yan wasan da suka fi fice a nahiyar Turai. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.