Isa ga babban shafi

Mbappe ya kafa tarihin jefa kwallaye mafi yawa a gasar duniya

‘Dan wasan gaba na kasar Faransa Kylian Mbappe ya kafa wani sabon tarihi na jefa kwallaye 3 a wasan karshe na cin kofin duniya, abinda ya kai yawan kwallayen da ya jefa a gasar da aka kammala a Qatar zuwa 8. 

Kyllian Mbappe
Kyllian Mbappe REUTERS - DYLAN MARTINEZ
Talla

A karawar da Faransa tayi da Argentina, Mbappe ya jefa kwallayensa guda 3 a mintina 80 da 81 da kuma 118 a wasan suka tashi 3-3, kafin ya kuma jefa kwallo guda a bugun daga kai sai mai tsaron gida. 

Abokin hamayyarsa Lionel Messi ya jefa kwallaye guda 2 ne a karawar, wadanda ya jefa a mintina 23 da 108, abinda ya kawo adadin kwallayensa a gasar zuwa 7, kafin sima ya jefa guda a bugun daga kai sai mai tsaron gidan bayan sun tashi wasan 3-3. 

Kwallayen da Mbappe ya jefa su suka taimakawa Faransa kai wasan zuwa bugun daga kai sai mai tsaron gida, a wasan da kasar Argentina sau biyu tana kama sahun gaba. 

Wadannan kwallayen da Mbappe ya jefa sun sanya shi cikin jerin manyan ‘yan wasan duniya da suka jefa kwallaye a gasar cin kofin duniya irin su Vava a shekarar 1958 da 1962 da Pele a shekarar 1958 da 1970, sai Paul Breitner a shekarar 1974 da 1982 sannan Zinedine Zidane a shekarar 1998 da 2006. 

A shekaru 23 Mbappe ya jefa kwallaye 15 a gasar cin kofin duniya a wasanni 17 da ya buga, wadanda suka zarce na zaratán ‘yan wasan Faransa irinsu Thierry Henry mai kwallaye 6 da Zinedine Zidane mai 5. 

Ya zuwa yanzu ‘dan wasan Jamus Miroslav Klose ke rike da tarihin jefa kwallayen da suka fi yawa wadanda suka kai 16 a gasa 4 da ya halarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.