Isa ga babban shafi

Giroud da Mbappe sun kai Faransa zagaye na gaba a gasar cin kofin duniya

Olivier Giroud ya zama dan wasan Faransa da ya fi kowa zura kwallo a raga a lokacin da kasar mai rike da kofin duniya ta yi waje da Poland inda suka kai wasan daf da na kusa da na karshe.

Olivier Giroud da Kylian Mbappé
Olivier Giroud da Kylian Mbappé REUTERS - DYLAN MARTINEZ
Talla

Dan wasan gaban na AC Milan ne ya ci wa Faransa kwallo ta 52 kenan da ya zurawa kasarsa, inda ya zarce Thierry Henry a yawan kwallon da ya ciwa Faransar.

Kwallon mai cike da tarihi ta zo ne bayan hutun rabin lokaci yayin da Giroud ya sarrafa ta.

Dan wasa Kyllian Mbappe ne ya zura kwallo kwallaye biyun, wanda hakan ya bawa Faransa damar jan ragamar wasan da ci 3-1.

Yanzu haka dai Mbaffe kwallaye biyar ya zurawa kasarsa tun daga fara gasar ta bana kawo yanzu.

Robert Lewandowski ya yi nasarar samun nasarar zura kwallo ga kasarsa Poland, bayan samun dama a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.