Isa ga babban shafi

Senegal ta tsallaka zagayen 'yan 16 a gasar cin kofin duniya

Kalidou Koulibaly ya tura Senegal zuwa zagayen ‘yan 16 a gasar cin kofin duniya a karo na biyu kacal a tarihinta bayan nasara da ta samu a wasan da suka doke Ecuador da ci 2-1 a ranar Talata.

Kalidou Koulibaly dan wasan Senegal kenan lokacin da yake murnar zuwa kwallo a ragar Ecuador
Kalidou Koulibaly dan wasan Senegal kenan lokacin da yake murnar zuwa kwallo a ragar Ecuador REUTERS - DYLAN MARTINEZ
Talla

Nasarar da Netherlands ta yi kan Qatar na nufin cewa nasara ce kawai za ta taimakawa Senegal ta tsallaka zuwa zagayen gaba a rukunin A.

Senegal ce ta fara zura kwallo ta hannun Ismaila Sarr a bugun daga kai sai mai tsaron gida, sai dai duk da cewa kyaftin din Ecuador Enner Valencia ya buya a wasan, dan wasan Brighton Moises Caicedo ya farke kwallon a minti na 67 kafin Koulibaly ya fitar da tawagarsa sannan Ecuador ta koma gida.

Kocin Senegal Aliou Cisse ya yi alkawarin kafin wasan cewa kwararrun ‘yan wasansa ba za su sassauta ba, kuma ‘yan Afirka ne suka nuna bajinta.

Ecuador ta fara wasan a zagaye na biyu cikin karsashi sannan kuma ta kara azama, watakila tana kokarin tabbatar da cewa mamayar da Netherlands ta yi kan Qatar na nufin sai ta dage wajen yin kunnen doki don wucewa mataki na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.