Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Magoya bayan Belgium sun kona motoci da fasa shaguna

'Yan sanda a Brussels sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare da ruwan zafi wajen tarwatsa masu zanga zanga a kasar Belgium bayan da Morocco ta lallasa kasar da ci 2-0 a gasar cin kofin duniyar dake gudana a Qatar.

Fusatattun masu zanga-zangar sun kone motoci da shagunan ne bayan da Morocco ta casa kasar a gasar cin kofin duniya da ke gudana a kasar Qatar
Fusatattun masu zanga-zangar sun kone motoci da shagunan ne bayan da Morocco ta casa kasar a gasar cin kofin duniya da ke gudana a kasar Qatar REUTERS - YVES HERMAN
Talla

Bayanai sun ce fusatattun mutane da dama suka shiga zanga zangar a birnin Brussels inda suka dinga fasa tagunan shaguna da jefa abin wasan wuta da kuma cinnawa motoci wuta.

'Yan sandan sun sanar da kama mutane 11 daga cikin wadanda suka shiga zanga- zangar saboda rashin samun nasarar da kasar tayi a wasan.

Mai magana da yawun 'yan sandan tace tarin mutane ne suka shiga zanga-zangar, wasu sanye da abin da ke rufe fuskokinsu, yayin da wasu kuma dauke da itatuwa suka kai hari akan jami’na tsaro tare da raunata wani dan jarida.

Magajin Garin Brussels, Philippe Close yayi Allah wadai da tashin hankalin a kasar dake dauke da 'yan assalin kasar Morocco sama da dubu 500.

A wani labari kuma, 'yan sanda a kasar Netherlands sun yi amfani da kulakai wajen tarwatsa magoya bayan Morocco bayan samun nasara a kan Belgium.

'Yan sandan sun ce sun tarwatsa akalla mutane 500 da suka yi gangami a tsakiyar birnin Rotherdam, baya ga wadanda suka fito a biranen Hague da Amsterdam da Utretch.

Jami’na tsaron sun ce magoya bayan Morocco sun harba abin wasan wuta da gilashi akan 'yan sandan wadanda suka mayar da martani da hayaki mai sa hawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.