Isa ga babban shafi

Jadawalin Gasar Zakarun Turai: Liverpool za su hadu da Real Madrid

A Litinin din nan ce dai aka hada yadda wasan zagaye na biyu na gasar zakarun nahiyar Turai zai kasance, inda aka fidda jadawalin wasannin da za a fafata a zagayen kungiyoyi 16 na gasar.

jadawalin zagayen kungiyoyi 16 na gasar zakarun nahiyar Turai.
jadawalin zagayen kungiyoyi 16 na gasar zakarun nahiyar Turai. © uefa.com
Talla

A hadin da aka yi, kungiyoyin da suka buga wasan karshe a gasar a shekarar da ta gabata Real Madrid da Liverpool za su hadu a wasan zagaye na biyu a bana.

RB Leipzing da ta kare a mataki na biyu a rukunin F za ta kara da Manchester City da ta jagoranci rukunin G, Club Brugge zata kara ne da Benfica, AC Milan ta karbi bakuncin  Tottenham.

Sauran wasannin sun hada da Eintracht Frankfurt ta hadu da Napoli, Borussia Dortmund da Chelsea, Inter da Porto, sai kuma wasa tsakanin PSG da Bayern Munich wanda ke cikin manyan wasannin da za’a buga a wannan zagayen.

A ranakun 14 da 15 da kuma 21 da 22 na watan Fabuwairun shekara mai zuwa ne za’a fara fafatawa a wasan farko na zagayen na biyu a gasar zakarun nahiyar Turai.

A bangaren gasar Europa kuwa, Barcelona da ta kare a mataki na uku a rukunin gasar zakarun nahiyar Turai, za ta kara ne da Manchester United, Juventus ta kara da Nantes sai Sporting Lisbon da Midtjylland.

Sauran wasannin gasar ta Europa sun hada da Shakhtar Donetsk da Rennes, Ajax da Union Berlin, Bayer Leverkusen da Monaco, Sevilla da PSV Eindhoven sai FC Salzburg da Roma.

A ranar 16 ga watan Fabuwairu ne za’a buga wasan farko na gasar ta Europa, sai kuma wasa na biyu a ranar 23 na Fabuwairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.