Rangers ta zama kungiya mafi gazawa a tarihin gasar zakarun Turai
Zakarar gasar kwallon kafar Scotland, Rangers FC ta zama kungiyar da ta fi kowacce rashin tabuka abin kirki a tarihin gasar zakarun Turai, sakamakon gazawarta a wasannin rukuni na gasar da aka kammala jiya talata.
Wallafawa ranar:
Wannan tarihi mai muni da Rangers ta kafa, ya biyo bayan nasarar da Ajax ta samu kanta da kwallaye 3-1, a wasan karshe na matakin rukunin da suka kara jiya Talata a gasar Zakarun Turai.
Sakamakon ya nuna kenan Rangers ba ta samu maki ko da guda ba rukuninta na A, bayan buga wasanni 6, yayin da aka jefa mata kwallaye 20 a raga.
Rangers, wadanda suka kai wasan karshe a gasar cin kofin Europa a kakar wasan da ta gabata, kwallo daya kacal suka samu jefawa a ragar abokan hamayya cikin wasanni 6 a gasar zakarun Turai ta bana.
Wannan rashin karsashi ya sanya Rangers zama kungiya mafi rashin kokari a matakin rukuni na gasar ta Zakarun Turai, tun lokacin da aka sake fasalin gasar a shekarar 1992.
A baya, kungiyar Dinamo Zagreb ta kasar Croatia ce ta ke rike wannan tarihin, bayan da ta kare a mataki na karshe a rukuninsu ba tare da maki ba, yayin da kuma aka jefa mata kwallaye 19 a raga, a kakar wasa ta 2011/12.
Ita ma Viktoria Plzen ta yi daidai da tarihin Dinamo Zagreb a ranar Talata da yamma yayin da ta kare a mataki na karshe a rukuni na uku ba tare da maki ba, tare da karbar bakuncin kwallaye 19 a ragar ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu