Isa ga babban shafi

Salah ya kafa tarihin cin kwallaye 3 cikin sauri a gasar zakarun Turai

Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya kafa tarihin shiga sahun wadanda suka yi nasarar zura kwallaye 3 a wasa guda cikin sauri a gasar cin kofin zakarun Turai, bayanda ya zura kwallayen 3 wato hattrick cikin mintuna 6 da shiga fili a karawarsu da Rangers daren jiya laraba.

Dan wasan gaba na Liverpool mohamed Salah bayan zura kwallaye 3 cikin mintuna 6 a wasansu da Rangers karkashin gasar cin kofin zakarun Turai.
Dan wasan gaba na Liverpool mohamed Salah bayan zura kwallaye 3 cikin mintuna 6 a wasansu da Rangers karkashin gasar cin kofin zakarun Turai. Action Images via Reuters - LEE SMITH
Talla

Kwallayen na Salah dai ya goge tarihin Bafetimbo Gomis na Lyon wanda ya taba nasarar zuwa kwallaye 3 cikin mintuna 8 yayin wasansu da Dinamo Zagreb a 2011 karkashin makamanciyar gasar

Yayin wasan na jiya da ya gudana a Ibrox Liverpool ta tashi wasa 7 da 1 ne tsakaninta da Rangers har gidanta kuma shi ne wasa na farko a cikin kakar nan da aka ga ‘yan wasan Liverpool na nuna bajinta irin wannan.

Har zuwa yanzu dai wasanni 4 kacal cikin 11 da Liverpool ta doka ne ta samu nasara, musamman a gasar firimiyar Ingila da yanzu haka kungiyar ke matsayin ta 10 da maki 10, dalilin da ke ci gaba da janyowa ‘yan wasan kakkausar suka daga magoya baya.

Tuni dai wasu masu sharhin wasanni suka fara shawartar kungiyar kan ta fara ajje Salah a benci yayinda wasu ke ganin kamata ya yi a rage albashin Vigil van Dijk wanda ya gaza katabus a wannan kaka, kuma ko a wasan na jiya Salah yana benci ne aka sauya shi inda ya samu nasarar zura kwallayen 3.

A bangaren Rangers wadda ke dawowa gasar ta cin kofin zakarun Turai karon farko bayan shekaru 12 har zuwa yanzu bata da maki ko guda yayinda ta sha ruwan kwallaye 16 inda mai horar da kungiyar Van Bronckhorst ke cewa mintunan wasan na jiya ya zame musu tamkar kwana da yini.

Sai dai duk da nasarar ta Liverpool kungiyar ta ci gaba da zama ta 2 a rukuninta, yayinda ta ke bukatar akalla canjaras da Ajax gabanin iya tsallakawa rukuni na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.