Isa ga babban shafi

Wasan Tennis: Rodger Federer ya sanar da yin ritaya

Fitaccen dan wasan tennis dan kasar Switzerland, Roger Federer, zai yi ritaya bayan gasar cin kofin Laver na mako mai zuwa.

Dan wasan Tennis Rodger Federer kenan
Dan wasan Tennis Rodger Federer kenan RODGER BOSCH / AFP
Talla

"Wasan cin kofin Laver da za a yi a mako mai zuwa a Landan zai zama taron ATP na karshe," a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Dan wasan mai shekaru 41, wanda ya lashe kofunan Grand Slam 20 bai taka leda ba tun bayan da ya yi rashin nasara a wasan daf da na kusa da na karshe a Wimbledon a shekarar 2021, bayan da aka yi masa tiyatar gwiwa ta uku a cikin watanni 18.

Shahararriyar 'yar wasan tennis Serena Williams itama ta rataye takalminta, bayan ficewarta a gasar US Open a zagaye na uku a wannan watan.

Federer ya ce jikinsa ya gaya masa cewa lokaci ya yi da ya kamata ya rataye takalmansa.

"Na yi aiki tukuru don ganin na cimma burika a wannan fagen wasa, “ a cewar Federer.

“Amma ni kuma na san iyawa da yanayin jikina, kuma sakonsa zuwa gare ni a kwanan nan ya fito fili.

“Ina da shekara 41. Na buga wasanni sama da 1500 sama da shekaru 24 kenan.

"Tennis ya ba ni kyauta fiye da yadda nake mafarki, kuma yanzu dole ne in gane cewa lokaci da ya kamata na dakata."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.