Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

FIFA ta amince da sake doka wasan Argentina da Brazil wanda aka dakatar a bara

Hukumar FIFA ta sanar da yiwuwar baiwa kasashen Brazil da Argentina damar doka wasansu na neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da ta dakatar a bara sakamakon takaddama kan karya dokokin yaki da covid-19 da ya kai ga rikici.

Rikicin da ya tilasta dakatar da wasan Argentina da Brazil cikin watan Satumban bara.
Rikicin da ya tilasta dakatar da wasan Argentina da Brazil cikin watan Satumban bara. AP - Andre Penner
Talla

Duk da cewa kasashen 2 dukkaninsu sun samu tikitin zuwa gasar ta cin kofin duniya da za ta gudana a Qatar a karshen shekarar nan, amma dukkaninsu sun suna bukatar doka wasan cikin takardun da suka aikewa FIFA.

A baya dai FIFA ta yi watsi da daukaka karar da kasashen 2 suka shigar don basu damar doka wasan da kuma janye tarar da aka lafta musu saboda takaddamar ta ranar 5 ga watan Satumban bara, wanda ya kai ga basu damar doka wasan a watan Fabarairu amma karkashin tsauraran sharudda da dukkaninsu suka ki amincewa.

An dai dakatar da wasan ne a wancan lokaci sakamakon shigar wasu ‘yan wasan Argentina 5 Brazil ba tare da killace kansu na tsawon kwanaki ba wanda kuma ya sabawa dokokin yaki da covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.