Isa ga babban shafi

Masar ta tuhumi Senegal da nunawa 'yan wasanta wariyar launi

Hukumar kwallon kafa ta Masar ta shigar da kara a hukumance kan Senegal inda ta ce jami’ai da ‘yan wasanta sun fuskanci cin zarafin wariyar launin fata da kuma firgitarwa a lokacin da suke shirin buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a ranar lahadi.

Tauraron kwallon kafar Masar Mohamed Salah a. tsakiyar 'yan wasan Senegal.
Tauraron kwallon kafar Masar Mohamed Salah a. tsakiyar 'yan wasan Senegal. © REUTERS/Amr Abdallah Dalsh/File Photo
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Instagram a ranar Talata, hukumar kwallon ta Masar ta ce tawagarta ta fuskanci cin zarafin ne bayan bayyanar wasu manyan rubuce-rubuce da aka yiwa 'yan wasa musamman Mohamed Salah, kyaftin dinsu.

Zalika an rika jifan ‘yan wasan na Masar  da kwalabe da duwatsu a lokacin da suke gudanar atasaye gabanin fara fafatawar da suka yi da takwarorinsu na Senegal.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, "An kai wa motocin bas din tawagar Masar hari, wanda ya yi sanadin farfasa tagoginsu tare da jikkata wasu mutane, abinda ya sanya su shigar da kara gaban hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF da kuma hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.