Buhari ya taya Senegal murnar lashe kofin Afirka
Shugaban Najeriya Muhammadu ya taya kasar Senegal murnar nasarar da ta samu a gasar cin kofin Afrika da aka kammala a Kamaru.
Wallafawa ranar:
Buhari ya mika sakon ne lokacin da ya karbi bakuncin Jakadan kasar Senegal a Najeriya, Babacar Ndiaye, a wani taron bankwana da aka yi a fadar gwamnati da ke Abuja jiya Alhamis, inda ya roke shi da ya mika sakon taya murna ga Shugaba Macky Sall kan nasarar da Teranga Lions suka samu a AFCON.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis mai taken, ‘Shugaba Buhari ya yi bankwana da jakadan Senegal, ya kuma taya kasar murnar nasarar da ta samu a AFCON.
Buhari ya kuma yi wa jakadan mai barin gado fatan samun nasara a duk inda zai yi aiki a gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu