Isa ga babban shafi
MEXICO - WASANNI

Mutane 26 sun jikkata a filin wasar Mexico

Akalla mutane 26 ne suka jikkata a lokacin da rikici ya barke tsakanin magoya baya a wani filin wasa na kasar Mexico ranar Lahadi.

'Yan wasan Mexico
'Yan wasan Mexico REUTERS/Jorge Silva
Talla

Rikicin sai da ya kai ga dakatar da wasar Liga MX tsakanin Queretaro da Atlas a mintuna na 63 a filin wasa na La Corregidora dake Santiago.

Wasu 'yan wasan sun yi yunkurin kwantar da hankalin magoya bayansu kafin a tura su dakin shirye-shirye.

Mutane 26 aka garzaya da su asibiti amma, 3 suka samu munanan raunuka.

Matakin da gwamnan jihar Queretaro, Mauricio Kuri yace abin takaici ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.