Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

PSG ta shiga rudu saboda rashin Messi, Mbappe

‘Yan wasan PSG 2 masu mahimmanci, Lionel Messi da Kylian Mbappe ba su kasance a filin atisaye ba ‘yan kwanaki gabanin wasanin da za su fafata da Lille ranar Juma’a da a gasar Ligue 1, da kuma RB Leipzig a gasar zakarun nahiyar Turai a Laraba mai zuwa.

PSG za ta buga wasanni biyu a 'yan kwanaki masu zuwa ba tare da  Messi da Mbappe.
PSG za ta buga wasanni biyu a 'yan kwanaki masu zuwa ba tare da Messi da Mbappe. FRANCK FIFE AFP/File
Talla

Babu wani karin bayani a game da rashin kasancewar Messi a filin atisaye a yau Alhamis, amma kuma an yi bayanin cewa takwaransa a kwallon kafa Kylian Mbappe yana fama da cutar kunne, hanci da makogoro.

Kafin ma yanzu, kungiyar da ke jan ragamar gasar ta Ligue 1 a Faransa tana jure rashin gogaggun ‘yan wasanta 3 Marco Verratti, Sergio Ramos da Leandro Paredes.

Jaridar L’Equipe ta Faransa ta ruwaito cewa lallai Mbappe ba zai buga wasannin ba, amma yiwuwar Messi ya murza tamaula kila wa kala ce.

PSG ta bada tazarar maki 7 a gasar  Ligue 1 bayan ta buga wasanni 11, kuma tana jan ragamar rukunin A a gasar zakarun Turai, inda ta ba Manchester City tazarar maki 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.