Messi ya ciwa PSG kwallo na uku a gasar zakarun Turai
Lionel Messi ya ci wa Paris St-Germain kwallaye biyu a karawar da ta doke RB Leipzig da ci 3-2 a gasar zakarun Turai ranar Talata.
Wallafawa ranar:
Kylian Mbappe ne ya fara ci wa PSG kwallo, Sai dai Andre Silva ya farke kwallon, sannan Nordi Mukiele ya kara na biyu, inda kungiyar ta Jamus ta shiga gaba. Daga bisani Messi ya farke wa PSG, sannan ya ya kara na uku a bugun fenariti.
PSG ta sake samun wani bugun finaretin ana daf da tashi wasa, amma sai Mbappe ya barar.
Messi ya yi wasa 123 a Champions League
Kawo yanzu Messi ya ci kwallo uku a PSG a Champions League, tun bayan da ya koma kungiyar, wanda ya ci daya a wasan da suka doke Manchester City 2-0. Kuma jummular kwallaye 123 Messi ya ci a gasar Zakarun Turai, kuma 120 ya zura su ne lokacin da yake wasa a tsohuwar kungiyarsa Barcelona.
Kyaftin din Argentina ya zama dan wasa na hudu da ya zura kwallo a wasa biyu a jere a PSG bayan Neymar da Alex da kuma George Weah.
Neymar bai buga wasa ba
Neymar bai buga wa PSG wasa ba, saboda rauni da ya samu yayin wasa da tawagar Brazil a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu