Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Messi ya zurawa PSG kwallon farko a wasansu da Manchester City

Sabon dan wasan da PSG ta saya daga Barcelona Lionel Messi ya yi nasarar zura kwallonsa na farko yayin haduwarsu da Manchester City a daren jiya talata, kwallon da ke matsayin ta 74 da tauraron na Argentina ya zura a karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai

Idrissa Gueye da Lionel Messi 'yan wasa biyu da suka cirewa PSG kitse a wuta yayin wasan na jiya.
Idrissa Gueye da Lionel Messi 'yan wasa biyu da suka cirewa PSG kitse a wuta yayin wasan na jiya. Alain JOCARD AFP
Talla

Tun farko Idris Gueye ya fara zurawa PSG kwallonta na farko gabanin Messi a zura ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a wasan wanda aka tashi PSG na da 2 Manchester City na nema.

Wasan na jiya dai shi ne na biyar da Messi ya dokawa sabuwar kungiyar tasa kuma minti na 264 a fili ba tare da kwallo ba gabanin nasarar kan Manchester City kungiyar da ke karkashin tsohon manajan Messin wato Pep Guardiola kocin da suka kafa gagarumin tarihi tare da dan wasan yayin taka leda a Barcelona.

A zantawarsa da manema labarai bayan kammala wasan, Messi ya tabbatar da cewa ya matukar kaguwa yaga kwallonsa ta farko a PSG bayan taka leda a jerin wasanni ba tare da kwallo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.