Isa ga babban shafi
Kasuwar hada-hadar 'yan wasa

Ba zan zauna a PSG ba ko da nawa zasu biya ni - Mbappe

Dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, yace ba zai sanya hannu a sabuwar kwangila da Paris St-Germain ba,  ko da nawa kungiyar dake  wasannin Ligue 1 za ta ba shi, saboda burins ana taka leda a Real Madrid.adrid. (AS - in Spanish)

Dan wasan Faransa da PSG Klian Mbappe.
Dan wasan Faransa da PSG Klian Mbappe. AP - Luca Bruno
Talla

Liverpool da Manchester City da Manchester United duk suna zawarcin dan wasan Monaco da Faransa Aurelien Tchouameni, mai shekara 21, wanda darajarsa ta kai kusan fan miliyan 40. (ESPN)

Manchester City na shirin maye gurbin dan wasan gaba na Ingila Raheem Sterling, mai shekara 26, da dan wasan Bayern Munich da Poland Robert Lewandowski, mai shekara 33. (Express)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya tabbatar da cewa dan wasan tsakiya na Ingila Jesse Lingard, mai shekara 28, bazai sabanta kwantaraginsa ba, sai har ya ci gaba da haskawa fiye da yanzu.(Evening Standard)

Wakilin Paul Pogba Mino Raiola ya yiwa Barcelona tayin dan wasan tsakiyar na Manchester United.

Kwantiragin dan wasan na Faransa mai shekaru 28 a Old Trafford na shirin karewa a bazara mai zuwa kuma Raiola ya kuma tuntubi Juventus, Paris St-Germain, Real Madrid da kungiyoyin Premier da dama. (ESPN)

Dan wasan gaba na Everton da Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 24, zai kasance babban dan wasan Arsenal a bazara mai zuwa. (Football.London)

Kocin Roma Jose Mourinho na da sha'awar sayo dan wasan Barcelona Riqui Puig, mai shekara 22.(Sport - in Spanish)

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.