Isa ga babban shafi
Wasanni

Benfica ta sake jefa Barcelona cikin tsaka mai wuya

Barcelona ta sake yin rashin nasara karo na biyu a jere yayin gasar cin kofin Zakarun Turai, bayan da a jiya Laraba Benfica ta lallasa ta da kwallaye 3-0 a birnin Lisbon.

Mai horas da Barcelona Ronald Koeman a yayin wasan da Benfica ta lallasa su da kwallaye 3-0.
Mai horas da Barcelona Ronald Koeman a yayin wasan da Benfica ta lallasa su da kwallaye 3-0. PATRICIA DE MELO MOREIRA AFP
Talla

Idan za a iya tunawa dai a filin wasa na Estadio da Luz da ke birnin na Lisbon, kungiyar Bayern Munich ta lallasa Barcelona da kwallaye 8-2 a wasan kwata final na gasar ta cin kofin Zakarun Turai a kakar wasan da ta gabata.

A halin yanzu Barcelona ba wai kawai ta yi rashin nasara bane sau biyu a jere, ta sha kayen ne a wasannin farko na matakin rukunin ba tare da cin kwallo ko da guda ba.

Ronald Koeman a filin wasa na birnin Lisbon, inda suka yi rashin nasara ta biyu a matakin rukuni na gasar Zakarun Turai.
Ronald Koeman a filin wasa na birnin Lisbon, inda suka yi rashin nasara ta biyu a matakin rukuni na gasar Zakarun Turai. PATRICIA DE MELO MOREIRA AFP

A halin da ake ciki dai muhawara kan makomar kocin Barcelona Ronald Koeman ta dawo sabuwa, sakamakon rashin nasarar da kungiyar ke ci gaba da fuskanta a wasannin da take bugawa musamman ma a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Jim kadan bayan tashi daga karawar da suka yi da Benfica a daren ranar Laraba, dan wasan tsakiya na Barcelona Frankie de Jong ya yi watsi da kiraye kirayen a kori kocinsu Koeman saboda abin kunyar da suke ci gaba da yi.

A cewar De Jong korar Koeman zai magance komai ba, illa dai su sake lale kan dabarunsu na sarrafa kwallon kafa zuwa samun nasara.

A cikin watan Satumba Ronald Koeman ya ce ba ya tsoron rasa matsayinsa na kocin Barcelona, ​​duk da kayen da suka sha a wasan da suka yi da Bayern Munich da 3-0 a gasar Zakarun Turai, a daidai lokacin tuni dangantakar Koeman da shugaban Barcelona Joan Laporta ta yi tsami, kuma a bangarensa Koeman ya ba da tabbacin cewar Laporta yayi kokarin lalubo wanda zai maye gurbinsa a watannin baya, sai dai yunkurin ya faskara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.