Isa ga babban shafi
Wasanni

Ba na fargaba kan makoma ta a Barcelona - Koeman

Ronald Koeman ya ce ba ya tsoron rasa matsayinsa na kocin Barcelona, ​​duk da kayen da suka sha a wasan da suka yi da Bayern Munich da 3-0 makon da ya gabata a gasar Zakarun Turai.

Mai horas da kungiyar Barcelona Ronald Koeman.
Mai horas da kungiyar Barcelona Ronald Koeman. AFP/File
Talla

Yayin wasan dai Barcelona ta gaza kai kwakkwaran hari ga ragar kungiyar Baryern.

Tuni dai dangantakar Koeman da shugaban Barcelona  Joan Laporta ta yi tsami a makwannin da suka gabata, kuma a bangarensa Koeman ya ba da tabbacin cewar Laporta yayi kokarin lalubo wanda zai maye gurbinsa a watannin baya, amma yunkurin ya faskara, abinda ya sanya har yanzu akwai rade-radin kowane lokaci daga yanzu yana iya rasa matsayin sa.

Rashin nasarar da Barcelona ta kara yi a hannun  Bayern Munich ya tabbatar da gibi mai fadi da ke tsakanin manyan kungiyoyin a nahiyar Turai, la’akari da lallasawar da Baryern ta yiwa Barcelonan da kwallaye 8-2, yayin wasan kwata final na gasar Zakarun Turan shekarar bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.