Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal ta zazzagawa Tottenham kwallaye uku cikin mintuna 35

Arsenal ta zazzagawa kungiyar Tottenham kwallaye uku cikin mintuna 35 a wasan gasar firimiyar da suka fafata jiya Lahadi, wanda daga karshe Arsenal din ta samu nasara da kwallaye 3-1.

Kocin Arsenal Mikel Arteta cikin farin ciki bayan nasarar lallasa kungiyar Tottenham da 3-1 a gasar Premier, ranar 26 ga Satumba, 2021 a filin wasa na Emirates da ke Landan.
Kocin Arsenal Mikel Arteta cikin farin ciki bayan nasarar lallasa kungiyar Tottenham da 3-1 a gasar Premier, ranar 26 ga Satumba, 2021 a filin wasa na Emirates da ke Landan. Ben STANSALL AFP
Talla

‘Yan wasan Arsenal Emile Smith Rowe, Aubameyang da kuma Bukayo Saka ne suka ci kwallayen 3, yayin da Song Heung-min ya ci wa Tottenham guda.

A makwanni uku da suka gabata dai, Tottenham na cikin kungiyoyin da ake saman teburin gasar Firimiyar Ingila, yayin da Arsenal ke zaman ta karshe ba tare da maki ko daya ba, bayan lallasan da aka sau uku jere da juna, a wasannin da ta fafata da Brentford, Chelsea da kuma Manchester City, mafi munin farkon kakar wasa da kungiyar ta Gunners ta gani cikin shekaru 67.

Bukayo Saka yayin murnar kwallon da ya jefa a ragar Tottenham.
Bukayo Saka yayin murnar kwallon da ya jefa a ragar Tottenham. Ben STANSALL AFP

Sai dai a halin yanzu Arsenal din ta farfado bayan lashe. wasanni uku a jere da suka hada da wanda ta doke, Norwich, da Burnley dukkaninsu da 1-0, sai kuma jiya da ta lallasa Tottenham da 3-1 abinda ya sa a yanzu ta koma ta 10 da maki 9.

A sauran wasannin karshen makon da aka buga a gasar Firmiyar ta Ingila dai, Manchester City ta doke Chelsea ta 1-0, abin da ya kawo karshen rashin shan kayen kungiyar ta Chelsea ta yi tun bayan fara kakar wasa ta bana.

Dan wasan Manchester City Gabriel Jesus yayin kokarin zura kwallo a ragar Chelsea yayin karawa a filin wasa na Stamford Bridge. Ranar 25 ga Satumban shekarar 2021.
Dan wasan Manchester City Gabriel Jesus yayin kokarin zura kwallo a ragar Chelsea yayin karawa a filin wasa na Stamford Bridge. Ranar 25 ga Satumban shekarar 2021. © Ben STANSALL AFP

Liverpool da Brentford sun tashi 3-3, yayin da Manchester United ta yi rashin nasara a fafatawar ta da Aston Villa da 1-0.

A wasu daga cikin wasannin La Liga a Spain kuwa, Sevilla ta doke Espanyol da 2-0, Real Madrid kuwa da kyar ta shay ayin karawa da Villareal inda suka tashi 0-0, yayin da Barcelona ta lallasa Levente da 3-0.

A gasar Ligue 1 ta Faransa PSG da har yanzu Lionel Messi bai samu ci mata kwallo ba, ta samu nasara kan Montpellier da 2-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.