Isa ga babban shafi
GASAR-PREMIER

Manchester City ta lallasa Arsenal da ci 5-0

Kungiyar Manchester City ta lallasa Arsenal da ci 5-0 a karawar da suka yi a gasar Firimiya ta Ingila, wanda shine kaye na 3 a jere da kungiyar Arsenal ta gani tun bayan bude fara sabuwar gasar bana.

Manajan Arsenal Mikel Arteta
Manajan Arsenal Mikel Arteta FACUNDO ARRIZABALAGA POOL/AFP
Talla

Ilker Gundogan ya fara jefawa Manchester City kwallon ta a minti 7 kacal da fara wasan, yayin da Tores ya jefa ta 2 a minti 12, sannan Gabriel Jesus ya jefa ta 3 a minti 43 kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Ana dawowa daga hutun rabin lokaci Rodri ya jefawa Manchester City ta 4, sannan Torres ya jefa ta 5 a minti 84, abinda ya baiwa City damar komawa saman tebur da maki 6 kafin sauran wasannin da za’a kara yau.

Dan wasan Arsenal da aka kora Granit Xhaka
Dan wasan Arsenal da aka kora Granit Xhaka Oli SCARFF AFP

Yayin gudanar da wasan an baiwa dan wasan Arsenal guda Granit Xhaka jan kati saboda laifin da ya aikata, abinda ya rage yawan Yan wasan kungiyar.

Tuni masu sha’awar kwallon kafa suka fara tsokaci dangane da makomar mai horar yan wasan Arsenal Mikel Arteta wanda ya gaza taka rawar gani tun bayan fara sabuwar kakar ganin yadda suka barar da maki 9 da kuma kasa jefa koda kwallo guda a raga.

Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar da masu sharhi na tsokaci dangane da bukatar sauya manaja Arteta domin maye gurbin sa da Antonio Conte, tsohon manajan Juventus wanda yanzu haka baya rike da wata kungiya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da abokan hammayar Arsenal irin su Manchester United da City da Chelsea da Liverpool ke taka rawar gani a gasar ta Firimiya, yayin da ita kuma yanzu haka ke matsayi na 20 a teburin gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.