Isa ga babban shafi
Wasanni

Gasar Zakarun Turai: An zazzaga kwallaye 28 cikin wasanni 8

Wasannin da aka fafata ranar Laraba a gasar Zakarun Turai sun dauki hankula masoya kwallon kafa sakamakon kayatarwar da suka yi, duk da cewar a bangaren wasu sakamakon wasannin bai yi musu dadi ba.

Jack Grealish yayin murnar cin kwallon sa ta farko a gasar Zakarun Turai, yayin karawar Manchester City da RB Leipzig da suka lallasa da 6-3.
Jack Grealish yayin murnar cin kwallon sa ta farko a gasar Zakarun Turai, yayin karawar Manchester City da RB Leipzig da suka lallasa da 6-3. Oli SCARFF AFP
Talla

A ranar ta Laraba dai jumillar kwallaye 28 aka ci a dukkanin wasanni 8 da aka fafata, kuma wasannin da aka fi jefa kwallaye a raga, sun hada da wanda Ajax ta lallasa Sporting CP daga kasar Portugal da kwallaye 5-1, sai Manchester City da ta doke RB Leipzig da 6-3, yayin da Liverpool ta samu nasara akan AC Milan da 3-2.

Dan wasan Liverpool Mohamed Salah yayin karawa da AC Milan a gasar Zakarun Turai.
Dan wasan Liverpool Mohamed Salah yayin karawa da AC Milan a gasar Zakarun Turai. Paul ELLIS AFP

‘Yan wasan Manchester City daban daban ne suka ci wa kungiyar ta su kwallaye 5 daga cikin 6 da ta samu, da suka hada da Nathan Ake, Riyad Mahrez, Jack Greelish, Joao Cancelo, Gebriel Jesus, yayin da Nordi Mukiele dan wasan RB Leipzig ya jefa kwallo a ragarsu bisa kuskure.

A sauran wasannin da aka kara, an tashi 1-1 tssakanin PSG da Club Brugge, 0-0 tsakanin Atletico Madrid da FC Porto, yayin da Borussia Dortmund ta doke Besiktas da 2-1.

A rukuni na 4 kuwa, FC Sheriff ta samu nasara kan Shaktar Donetsk da 2-0, yayin da Real Madrid ta sha da kyar a karawar ta da Inter Milan da 1-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.