Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Najeriya za ta hadu da Masar a rukuni guda na gasar cin kofin Afrika

Hukumar kwallon kafar Afrika ta fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar da za ta gudana a shekarar 2022, gasar wadda Kamaru za ta karbi bakoncin ta kunshi kasashen nahiyar ta Afrika 24.

Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika Patrice Motsepe.
Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika Patrice Motsepe. AP - Themba Hadebe
Talla

Gasar wadda yanzu ya ragewa kwanaki 144 gabanin fara dokata wadda kuma ita ce karo na 33 da kassahen na Afrika za su kara da juna, za ta faro ne daga ranar 9 ga watan Janairun 2022 zuwa 6 ga watan Fabarairun shekarar.

Jadawalin na CAF na nuna cewa rukunin farko wato A na dauke da kasashen Kamaru mai masaukin baki, kana Burkina Faso da Habasha da kuma Cape Verde.

Sai rukunin B da ya kunshi Senegal jagorar kwallon kafa a Afrika, kana Zimbabwe da Guinea da kuma Malawi.

Akwai rukunin C da ke kunshe da kasashen Morocco da Ghana da tsibirin Comoros da kuma Garbon.

Sannan rukunin D wanda ke dauke da Najeriya da Masar da Sudan da kuma Guinea Bissau.

Rukunin E na gasar na kunshe da Algeria mai rike da kambu da Sierra Leone da Equatorial Guinea da kuma Cote D’Ivoire.

Sai kuma rukunin karshe na F da ke dauke da kasashen Tunisia da Mali da Mauritania da Gambia.

Jadawalin na CAF ya nuna Super Eagles wadda ta dage kofin har sau 3 a tarihi amma ta kwana biyu ba tare da kawo shi gida ba za ta hadu da Masar wadda ta taba dage kofin sau 7 kuma ta ke matukar yunwarsa, wanda ke nuna akwai gagarumin aiki a gaban tawagar ta Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.