Isa ga babban shafi
Wasanni

Cutar Korona ta tilasta sauya lokacin karawar Fury da Wilder

Fitaccen dan wasan damben zamani na boxing dan kasar Birtaniya Tyson Fury, ya kamu da cutar Korona, abinda ya tilastawa masu shirya wasannin na boxing sauya lokacin karawar da aka shirya Furyn zai da Deontay Wilder daga ranar 24 ga watan Yulin da muke zuwa 9 ga watan Oktoba.

Tyson Fury da Deontay Wilder yayin karawa a gasar Damben Boxing.
Tyson Fury da Deontay Wilder yayin karawa a gasar Damben Boxing. AFP/File
Talla

Sai dai cikin sanarwar da masu shirya wasannin damben suka fitar a ranar Alhamis ta ce fafatawar tsakanin Wilder da Fury za ta gudana ne a filin dambe na T-mobile Arena dake birnin Las Vegas a Amurka kamar yadda aka tsara da fari.

A shekarar 2018 karfi ya zo daya yayin karawar da aka yi tsakanin Fury da Wilder, abin da ya baiwa Wilder damar ci gaba da rike kambinsa na WBC ajin masu nauyi.

Sai dai a watan Fabarairun shekarar 2020, Fury ya samu  doke Wilder a zagayen turmi na 7, nasarar da ta bashi damar karbe kambin na WBC da ya rasa a 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.