Isa ga babban shafi
Wasanni

Na fi kowa iya dambe a duniya - Kamaru Usman

Tauraron Damben Duniya Kamaru Usman ya yi nasarar kare kambinsa na ajin masu matsakaita dambe a karawar da suka yi da Jorge Masvidal abin da ya sa ya bayyana kansa a matsayin wanda yafi kowa iya dambe a duniya a wannan zamani.

Dan Najeriya  Kamaru Usman, wanda ya lashe kambin damben ajin matsakaita.
Dan Najeriya Kamaru Usman, wanda ya lashe kambin damben ajin matsakaita. Stephen R. Sylvanie/Reuters
Talla

Yayin karawar da Kamaru yayi da Masvidal wanda a karon farko aka bar 'yan kallo suka shiga a Jacksonville da ke Florida, dan Najeriyan ya doke BaAmurken da ya kalubalance shi, Jorge Masvidal a minti guda da dakikoki biyu na zagaye na biyu na karawar, abin da ya sa ya  shaida wa 'yan damben da ke wurin cewar yana ci gaba da murmurewa.

Wannan shi ne karo na 18 da Kamaru Usman ke samun nasara a jerin damben da ya ke fafatawa ba tare da an samun galaba a kan sa ba, abind a ya sa shi shelar cewar a yau ya zama dan damben da ya fi kowa a duniya.

Kafin dai wannan karawar, Kamaru da Masvidal sun kara a watan Yulin bara, inda dan Najeriyan ya doke abokin karawar ta shi a zagaye na 5.

Wannan ne karo na farko da aka yi wa Masvidal bugu guda a tarihin karawar damben sa wanda yawan su ya kai karawa 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.