Isa ga babban shafi
Wasanni - Ingila

Wariya ga 'yan wasan Ingila 3 ya fusata hukumar kwallon kafar kasar

Mai horar da kungiyar kwallon kafar Ingila Gareth Southgate ya koka da kalaman wariyar da wasu daga cikin ‘yan wasansa suka fuskanta yayin wasansu na jiya da suka yi rashin nasara a hannun Italy.

Bukayo Saka bayan rashin nasara a bugun fenariti.
Bukayo Saka bayan rashin nasara a bugun fenariti. Paul ELLIS POOL/AFP
Talla

A cewar Southgate nuna wariya ba dabi’a ce da ta dace da masoya kwallo ba, a don haka dole ne a dauki matakin ladabtar da wadanda ke da hannu a cin mutuncin ‘yan wasan 3.

‘Yan wasan Ingila da suka kunshi Marcus Rashford da Jadon Sancho da Bukayo Saka sun gamu da wariyar ne a shafukan sada zumunta, bayan rashin nasararsu a bugun fenaritin da aka yi tsakanin Ingilar da Italy wanda Italy ta doke tawagar ta 3Lions tare da dage kofin na Euro.

Sai dai duk da yadda wasu daidaiku ke ci gaba da furta kalaman wariya da na cin mutunci ga ‘yan wasan 3, kocin na Ingila ya basu kwarin gwiwar tunkarar kowanne kalubale, yayinda a bangare guda Jude Bellingham ya wallafa hoton ‘yan wasan 3 a shafinsa tare da rubutu a kasa da ke cewa muyi nasara tare haka zalika rashin nasara.

Tuni shima Firamninista Boris Johnson da hukumar kwallon kafar kasar suka tir da wariyar yayinda jami’an tsaro ke ci gaba da bincike don gano masu hannu a ciki da nufin hukunta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.