Ingila za ta doka wasan karshe karon farko bayan 1966
Kwallon karshe da Harry kane ya zura a kurarren lokaci bayan samun bugun daga kai sai mai tsaron raga ya bai wa Ingila nasarar lallasa Denmark da kwallo 2 da 1, wanda ke nuna tawagar ta 3 Lions ta samu sukunin kai wa wasan karshe karon farko cikin shekaru 55, inda za ta kara da Italiya wadda ta fitar da Spain a wasansu na shekaran jiya.
Wallafawa ranar:
Tun a minti na 30 Denmark ta zura kwallonta ta farko ta hannun dan wasanta Mikkel Damsgaard ko da ya ake ingilar ta farke tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci amma fa ta hanyar kuskuren kwallon da Simon Kjaer ya zurawa kasarsa da kansa, gabanin samun bugun fenaritin da Harry Kane ya zura kwallo a mintin karshe.
Wasan wanda ya gudana a filin Wembley da ke London gaban ‘yan kallo kusan dubu 60 magoya baya sun barke da sowa tare da rungumar juna ba tare da tunanin matakan hana yaduwar corona, saboda murnar kaiwa matakin wanda rabon Ingila da shi tun kafin a haifi kowanne daga cikin ‘yan wasan na ta har ma da shi kansa kocin Gareth Southgate mai shekaru 50.
Ba kadai wadanda ke cikin filin na Wembley ba daren na jiya ya zama gagarumin biki ga iyalai da dama a kasar inda inda aka kwana ana shagugulan nasarar wasa.
Tsohon Dan wasan gaba na Ingila da ke cikin tawagar da doka gasar cin kofin Duniya ta 1966 da Ingilar ta yi nasara kan Jamus Gary Lineker ya ce bai yi tunanin yana da dacen sake ganin kasarsa a wasan karshe karkashin wata babbar gasa ta Duniya ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu