Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Denmark na fargabar Harry Kane a haduwarta da Ingila

Gabanin karawarsu ta yau laraba, mai horar da tawagar kwallon kafar Denmark Age Hareide ya yi ikirarin cewa kwazo da bajintar dan wasan gaba na Ingila Harry Kane ya wuce yadda mutane ke tsammani, domin kuwa a cewarsa yanzu haka dan wasan mai shekaru 27 sai dai a kwatantashi da Cristiano Ronaldo na Portugal.

Dan wasan gaba na Ingila Harry Kane.
Dan wasan gaba na Ingila Harry Kane. Pool via REUTERS - MATTHEW CHILDS
Talla

A cewar Age, tabbas su na fargbar Kane a filin wasa yayin karawar ta su, yana mai cewa idan akwai dan wasan da zai iya kai tawagar ta Ingila ga nasara akan Denmark ba kowa ba ne face Kane.

Da misalin karfe 8 na daren yau ne kasashen biyu na Denmark da Ingila za su kara da juna a wasan gab da na karshe na cin kofin EURO, wasan da zai gudana a filin wasa na Wembley da ke tsakar London, kuma zai zama irinsa na farko da Ingila ke fatan ganin ta tsallake shi don kaiwa wasan karshe tun bayan gasar cin kofin Duniya a shekarar 1966.

Mai horar da tawagar ta Denmark ya ce Kane na da hadari kwatankwacin Ronaldo a filin wasa wanda dama kadan ya ke ya zura kwallo, a don haka za su wasa da taka-tsan-tsan don kaucewa illar da zai iya yi musu.

Duk da cewa Harry Kane bai zura ko da kwallo guda ba a wasannin Ingila matakin rukuni, amma ya ratata kwallayen da ya bai wa kasar damar yin waje da Jamus da kuma Ukraine daga gasar a matakin wasannin rukunin ‘yan 16 da kuma ‘yan 8.

Duk dai wadda ta yi nasara a karawar ta yau tsakanin Denmark da Ingila kai tsaye za ta hadu da Italy a wasan karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.