Isa ga babban shafi
Wasanni - Gasar Cin Kofin Turai

Euro 2020: Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare

‘Yan wasan tawagar kwallon kafar Ingila na ci gaba da kintsawa haduwarsu da Italiya a wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Turai a ranar Lahadi mai zuwa, inda suke fatan samun nasarar lashe kofi na farko cikin shekaru 55.

'Yan wasan Ingila dake wakiltar kasar a gasar cin kofin kasashen Turai.
'Yan wasan Ingila dake wakiltar kasar a gasar cin kofin kasashen Turai. © AFP - GLYN KIRK
Talla

Rabon da Ingila ta lashe wani gagarumin kofi tun shekarar 1966, lokacin da ta lashe gasar cin kofin duniya.

Ingilar ta samu gurbi a wasan karshen ne bayan doke Denmark da ci 2-1 a Wembley a gaban magoya bayanta fiye da dubu 50 a ranar Laraba.

Rahotanni na cewa, akalla ‘yan kallo dubu 60 za su yi dandazo domin kashe kwarkwatar idonsu a wasan karshen a Wembley a ranar Lahadi, yayin da wasu rahotanni ke cewa, da yiwuwar adadin ‘yan kallon ya kai dubu 90.

Filin wasa na Wembley dake birnin London.
Filin wasa na Wembley dake birnin London. Adrian DENNIS AFP/File

Manazarta lamurran kwallon kafa dai na kallon akwai jan aiki a gaban Ingila kafin lashe kofin gasar ta Euro 2020 la’akari da cewar Italiya a yanzu na kan  ganiyarta ta taka leda tun bayan da ta dauki darussa daga sakacinta na rasa gurbi a gasar cin kfion duniya ta 2018.

Italiya ta buga wasanni 33 a jere ba tare da an samu nasara a kanta ba, sannan kuma tun farkon bude gasar ta Euro 2020, ta fara nuna bajinta a wasanta na farko da Turkiya da ta lashe da 3-0.

Kazalika Italiya ce, ta fitar da Belgium daga gasar ta cin kofin kasashen Turai, duk da cewa, Belgium ce ke jan ragama a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Turan.

'Yan wasan Italiya yayin murnar kaiwa zagayen wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Turai bayan fitar da kasar Spain daga gasar a filin wasa na Wembley.
'Yan wasan Italiya yayin murnar kaiwa zagayen wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Turai bayan fitar da kasar Spain daga gasar a filin wasa na Wembley. JUSTIN TALLIS POOL/AFP

Har ila yau, Italiyar ce doke Spain wadda ta lashe gasar cin kofin kasashen Turan sau 3.

Tarihi dai ya nuna cewar sau 27 aka taba fafatawa tsakanin Italiya da Ingila a wasanni daban daban da suka fafata, inda Italiya ta samu nasara a wasanni 11, Ingila ta samu nasara a guda 8, suka kuma yi canjaras ko kunnen doki a ragowar wasannin 8.

Duba da wadannan alkaluma, ana iya cewa, lallai sai Ingila da zage damtse sosai kafin ta samu nasarar casa Italiya a wasan karshe.

Daga cikin kalubalen da Ingila za ta fuskanta, har da  jajircewa daga bangren ‘yan wasan bayan na Italiya irinsu Giorgio Chiellini da Leonardo Bonucci da tauraruwarsu ta haska sosai a gasar ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.