Isa ga babban shafi
Wasanni - Kwallon Kafa

Italiya ta wahala kafin kaiwa wasan karshe na Euro 2020 - Mancini

Mai horas da tawagar kwallon kafar Italiya Roberto Mancini ya ce shakka babu sun sha wahala matuka kafin samun nasarar doke Spain domin kaiwa zagayen wasan karshe.

Mai horas da tawagar kwallon kafar kasar Italiya Roberto Mancini.
Mai horas da tawagar kwallon kafar kasar Italiya Roberto Mancini. Handout via REUTERS - HANDOUT
Talla

Tuni dai shi ma fitaccen dan wasan kasar ta Italiya Leonardo Bonucci ya bi sawun kocin nasu wajen bayyana wahalar da suka sha a wasan na jiya.

A cewar Bonucci fafatawarsu da Spain shi ne wasa mafi wahala da ya buga a tsawon lokacin da ya shafe yana haskawa a kwallon kafa.

A jiya Talata ne dai Italiya ta samu nasara kan Spain da kwallaye 4-2 a matakin bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da suka tashi 1-1 a tsawon mintuna 90 da karin lokacin wasu mintunan 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.