Ronaldo ya rusa tarihin Platini a gasar cin kofin Turai
Cristiano Ronaldo ya zama dan wasan da ya fi kowa zira kwallaye a tarihin gasar cin kofin Turai yayin da Portugal ta doke Hungary da ci 3-0 a gaban magoya baya sama da dubu 60 a Budapest, yayin fafatawar da sukayi a ranar Talata.
Wallafawa ranar:
A mintuna na 87 Ronaldo ya ci kwallon farko a bugun fanareti, wanda kuma shine na 10 a gasar, inda ya zarta Michel Platini na kasar Faransa dake da tarihin kwallaye tara a gasar ta Turai.
Sai kuma ana daf da Karkare wasa, wato a mintuna na 90, yayi lale daf da mai tsaron ragar Hungary Peter Gulacsi, ya ciwa Portugal kwallonta na uku a wasan, wato kwallon sa na biyu, kuma na 11 a gasar.
Hungary ta yi kokarin ganin an tashi kunnen doki tsakaninta da mai rike da kambun, amma hakar ta bata cimma ruwa ba, akayi mata ruwan kwallaye har uku ana daf da Karkare wasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu