Isa ga babban shafi
Wasanni - Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta gargadi Rohr kan banbanta 'yan wasan gida da na ketare

Ministan harkokin wasanni na Najeriya Sunday Dare, ya gargadi kocin tawagar kwallon kafar kasar ta Super Eagles Gernot Rohr da ya daina kaskantar da darajar ‘yan wasan dake taka leda a kungiyoyin dake cikin kasar ta Najeriya.

Mai horas da tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles Gernot Rohr.
Mai horas da tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles Gernot Rohr. AFP/File
Talla

Ministan yayi wannan gargadi ne a yayin ziyarar da ya kaiwa sansanin atasayen ‘yan wasan Najeriya na cikin gida a Abuja, inda suke shirye-shiryen karawa da kasar Mexico a wasan sada zumuncin da zai gudana a ranar 3 ga watan Yuli.

Dare ya bayyana bacin ran rashin samun mai horas da tawagar kwallon Najeriyar ta Super Eagles a sansanin atasayen na Abuja, abinda ya ce ba za a lamunta ba.

A makon da ya gabata ne dai, Gernot Rohr yace ‘yan wasan Super Eagles din dake taka leda a kungiyoyin dake Najeriya ba za su iya samun nasara a wasan da za su kara da Mexico ba, furucin da ya bata ran wasu da dama ciki har da wasu tsaffin ‘yan wasan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.