Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Bruno Fernandez ya sake lashe kyautar gwarzon shekara na United

Dan wasan tsakiya na Manchester United Bruno Fernandez ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kungiyar na shekarar bana.

Gwarzon shekarar 2021 na Manchester United, Bruno Fernandez.
Gwarzon shekarar 2021 na Manchester United, Bruno Fernandez. © Pool via REUTERS/Shaun Botterill
Talla

Karo na biyu kenan a jere da dan wasan ke lashe wannan kyauta duk da cewar a watan Janairun 2020, ya kulla yarjejeniya da United daga kungiyar Sporting Lisbon.

Cikin sanawar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, Manchester United tace Bruno Fernandez ya lashe kyautar gwarzon nata na bana bayan samun mafi rinjayen kuri’un da magoya bayan kungiyar suka kada daga kasashe fiye da 200, abinda ya bashi nasarar doke Edinson cavani da kuma Luke Shaw.

A wannan kakar wasa, kwallaye 18 gwarzon na United ya ci cikinsu har da 9 a gasar Europa, yayin wasanni 36 da ya buga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.