Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

City, United da Chelsea na takara kan Harry Kane

Manchester City, da Manchester United da kuma Chelsea sun tuntubi wakilan tauraron Tottenham Harry Kane kan neman kulla yarjejeniya da shi, bayan da dan wasan ya shaidawa kungiyar tasa aniyarsa ta sauyin sheka a karshen kakar wasa bana.

Tottenham striker Harry Kane
Tottenham striker Harry Kane Shaun Botterill POOL/AFP
Talla

Yayin ganawar da yayi da manema labarai a baya bayan nan, Harry Kane mai shekaru 27 ya ce babban burinsa a yanzu shi ne neman lashe kofuna.

Bayanai sun ce tun a shekarar bara Kane ya so rabuwa da Tottenham, amma shugabannin kungiyar suka rarrashi shi ya kara lokaci, bayan da suka maye gurbin tsohon kocinsu Mauricio Pochettinho da Jose Mourinho, wanda shi ma suka sallama a watan jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.