Isa ga babban shafi
Wasanni - kwallon kafa

Zanga-zangar magoya bayan United ta tilasta ɗage wasanta da Liverpool

Zanga zangar da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United suka yi saboda nuna bacin ran su da yadda iyalan gidan Glazier ke tafiyar da ita, ta tilasta soke karawar da aka shirya kungiyar zata yi da Liverpool a gasar Firimiya ta Ingila.

Magoya bayan Manchester United dake zanga-zanga a filin Old Traford 2 ga watan Mayu 2021
Magoya bayan Manchester United dake zanga-zanga a filin Old Traford 2 ga watan Mayu 2021 Oli SCARFF AFP
Talla

Daruruwan magoya bayan kungiyar ne suka yi tattaki zuwa cikin filin kwallon Old Trafford domin nuna bacin ran su, inda suka dinga bayyana bukatar su ta korar Galzier.

Wasu tarin masu zanga zangar sun yi gangami a wajen filin wasan, kuma rahotanni sun ce an samu arangama tsakanin su da 'Yan Sanda wadanda suka nemi tarwatsa su.

Magoyabayan Manchester United dake zanga-zanga a filin Old Trafford 2 ga watan Mayu 2021
Magoyabayan Manchester United dake zanga-zanga a filin Old Trafford 2 ga watan Mayu 2021 Oli SCARFF AFP

Kungiyar ta sanar da cewar sakamakon ganawar da suka yi da jami’an Yan Sanda da Hukumar kula da gasar Firimiya da Majalisar Trafford da kuma kungiyoyin kwallon kafar, an dage karawar da aka shirya tsakanin Manchester United da Liverpool.

Sanarwar tace magoya bayan kungiyar na nuna kaunar su gare ta, kuma suna goyan bayan su wajen bayyana ra’ayin su cikin zanga zangar lumana.

Magoya bayan Manchester United dake zanga-zanga a filin Old Trafford, 2 ga watan Mayu 2021
Magoya bayan Manchester United dake zanga-zanga a filin Old Trafford, 2 ga watan Mayu 2021 Oli SCARFF AFP

Zanga-zangar ta tilasta daga wasa

Sai dai kungiyar ta bayyana bacin ran ta da kutsen da magoya bayan suka yi wanda ya tilasta dage karawar yau da kuma jefa rayuwar wasu yan kallo da ma’aikata da kuma Yan Sanda cikin hadari.

Magoya bayan Manchester United na korafi kan kin baiwa kungiyar isassun kudade wajen ganin ta sayi yan wasan da suka dace domin fafatawa da takwarorin ta na Ingila da Turai a gasar cin kofin zakarun nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.