Manchester United ta sake karbe jagorancin gasar Premier
Manchester United ta sake karbe jagorancin gasar Premier Ingila bayan da ta doke Fulham har gida da 2-1, yayin fafatawar da suka yi a daren ranar Laraba.
Wallafawa ranar:
Kungiyar Fulham ce ta soma jefa kwallo, kafin daga bisani United ta rama ta kuma kara guda ta hannun ‘yan wasanta Edinson Cavani da kuma Paul Pogba.
A yanzu Manchester United ke jagorancin gasar Premier da maki 40, Manchester City da a itama a ranar Laraba ta doke Aston Villa da 2-0 na biye da maki 38 a matsayi na biyu sai kuma Leicester City itama da maki 38 a matsayi na 3, yayin da Liverpool ke da maki 34.
A yau Alhamis ne kuma Liverpool din za ta kara da Burnley.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu