Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester United ta tsallaka zagayen daf da na kusa da na karshe a kofin Kalubale

Manchester United ta tsallaka zuwa wasan daf da na kusa da na karshe na gasar neman cin kofin kalubale, bayan doke West Ham da ci 1 mai ban haushi.

'Yan wasan Manchester United yayin murnar doke West Ham a gasar Premier Ingila da suka haye zagayen daf da na kusa da na karshe
'Yan wasan Manchester United yayin murnar doke West Ham a gasar Premier Ingila da suka haye zagayen daf da na kusa da na karshe REUTERS/Phil Noble
Talla

Bayan wannan nasara ne manajan club din Ole Gunnar Solskjaer ya gargadi ‘yan wasan da su kara azama, duba da cewar basu taka rawar gani ba a filin Old Trafford da dusar kankara ta mamaye.

To sai dai kwallon daya da Scott Mak-Tominay ya zura a ragar West Ham a mintuna na 96, wato bayan karin lokaci ya tabbatar da nasarar United na tsallakawa zuwa zagayen kungiyoyi takwas na karshe a kaka ta bakwai a jere.

Rabon United ta dauki Kofin FA tun a shekarar 2016, amma kwallaye uku da Mak-Tominay ya ci a wasanni uku, ya karawa kungiyar damar ci gaba da farautar daukar kofin a karo na 13.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.