Zakarun Turai: Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare
Yau Talata 13 ga watan Afrilu za a cigaba da fafatawa a gasar cin kofin zakarun Turai tsakanin kungiyoyi 8 a zagayen kwata final.
Wallafawa ranar:
Wasannin da za a buga a yau din dai na matsayin zango biyu, bayan wadanda suka gudana a makon jiya.
Chelsea za ta fafata da FC Porto, inda za take fatan maimaita samun nasarar da ta yi a zagayen farko na doke Porto da 2-0.
Wasa na biyu da za a fafata kuma shi ne tsakanin PSG da Bayern Munich, wanda a zagayen farko PSG ce ta samu nasara da 3-2.
Wasan na yau tsakanin PSG da Bayern Munich dai zai dauki hankali, la’akari da cewar dukkaninsu ba kanwar lasa bane, la’akari da bajintar da suka nuna a bana, da kuma gasar Zakarun Turan ta bara da suka fafata a wasan karshe, inda Munich ta samu nasara da 1-0.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu