Isa ga babban shafi
Wasanni-Liverpool

Abu ne mai sauki Liverpool ta iya sauya nasarar Real Madrid- Lawrenson

Tsohon dan wasan Liverpool Mark Lawrenson, da ya taka leda da kungiyar matsayin mai tsaron baya tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980 ya ce sam ba abin mamaki bane idan Liverpool ta sauya nasarar Real Madrid a haduwarsu ta makon gobe, domin kuwa a cewarsa tawagar ta yi kaurin suna wajen iya hakan.

Tawagar Liverpool bayan shan kaye hannun Real Madrid da kwallaye 3 da 1.
Tawagar Liverpool bayan shan kaye hannun Real Madrid da kwallaye 3 da 1. GABRIEL BOUYS AFP
Talla

Tsohon mai tsaron bayan na Liverpool Lawrenson ya bayyana cewa wasan na makon gobe ba zai zowa Real Madrid a yadda ta ke tunani ba domin kuwa komi zai iya faruwa a Anfield.

Sai dai kalaman na Lawrenson ya zo a wani yanayi da Liverpool ta fara manta yadda ake nasara a cikin gida domin kuwa rabonta da nasara a Anfield tun ranar 16 ga watan Disamban bara wato wasan da ta lallasa Tottenham.

Zuwa yanzu dai wasanni 6 Liverpool ta rasa a jere a Anfield din yayinda kuma ta iya zura kwallaye 2 tal a dukkanin wasan da ta yi cikin filin daga bara zuwa yanzu.

Sai dai a bangare guda idan aka kwatanta yadda tawagar ta yi kaurin suna wajen juya sakamako musamman a irin wannan mataki za a iya cewa komi zai iya faruwa, la’akari da irin bajintar da ta nuna a kakar wasa biyu da ta gabata, wato lokacin da ta sha kwallaye 3 da banza a gidan Barcelona amma kuma bayan mako guda ta ratatawa Barcelonar kwallaye 4 da banza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.