Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa-Turai

Mbappe ya nuna wa Bayern Munich iyakarta

Kylian Mbappe ya zura kwallaye biyu a wasan da kungiyarsa ta PSG ta nuna bajinta har ta doke Bayern Munich mai rike da gambi da ci 3-2 a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, matakin kwata fainal.

Kylian Mbappe tare da abokan taka ledarsa na murnar samun nasara kan  Bayern Munich
Kylian Mbappe tare da abokan taka ledarsa na murnar samun nasara kan Bayern Munich Christof STACHE AFP
Talla

Kungiyoyin biyu, su ne suka fafata a wasan karshe na gasar a bara, amma Beyern Munich ce ta samu nasarar dage kofin a wancan lokaci

Kodayake masharhanta na cewa, rashin dan wasan gaba na Beyern Munich, Robert Lewandowski wanda ke jinyar rauni, ya taimaka wa PSG wajen samun nasara.

Bayern Munich ta yi barin damammakin zura kwallaye a raga har sau 31.

Kazalika alkaluma sun nuna cewa, Bayern Munich ta fi rike kwallo da kashi 64, inda PSG ke da kashi 36.

Bayern Munich ta buga wasanni har guda 19 a Gasar Zakarun Turai a jere ba tare da shan duka ba, amma PSG ta karya mata lago a ranar Laraba.

Ita ma FC Porto ta sha kashi a hannun Chelsea da ci 2-0 a matakin wasan na dab da na kusan karshe a gasar.

Nasarar da Chelsea ta samu ya rage mata radadin dukan-kawo wukan da West Brom ta yi mata da ci 5-2 a gida  a gasar firimiyar Ingila a ranar Asabar da ta gabata.

Mason Mount da ya ci wa Chelsea kwallon farko a wasan, ya  kafa tarihin zama dan wasa mafi karancin shekaru a Chelsea da ya zura kwallo a gasar zakarun Turai domin kuwa ya zura kwallon ne yana da shekaru 22 da kwanaki 87 da haihuwa.

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya ce, sun yi farin ciki amma ba sosai ba, ganin cewa, akwai haduwar da kungiyoyin biyu za su sake yi a ranar Talata mai zuwa, kuma komai na iya faruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.