Isa ga babban shafi
Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Ina da kwarin gwiwa Messi ba zai sauya sheka ba - Koeman

Mai horas da Barcelona Ronald Koeman, ya bayyana kwarin gwiwar cewa kaftin din ‘yan wasansa Lionel Messi ba zai sauya sheka ba, saboda ficewarsu daga gasar Zakarun Turai, bayan rashin nasara a hannun PSG da 5-2.

Kaftin din Barcelona Lionel Messi tare da kocinsa Ronald Koeman bayan samun nasarar doke kungiyar Rayo Vallecano a zagayen da ya kunshi kungiyoyi 16 na gasar Copa del Rey. 27/1/2021.
Kaftin din Barcelona Lionel Messi tare da kocinsa Ronald Koeman bayan samun nasarar doke kungiyar Rayo Vallecano a zagayen da ya kunshi kungiyoyi 16 na gasar Copa del Rey. 27/1/2021. AP - Manu Fernandez
Talla

Har yanzu dai Messi ya ki sabunta yarjejeniyarsa da Barcelona, abinda ya sake haifar da shakku kan makomarsa a kungiyar.

A kakar wasan da ta gabata batun rabuwar Messi da Barcelona yayi karfi matuka, inda aka rika alkanta dan wasan da komawa Manchester City da wasu manyan kungiyoyi a Turai ciki har da PSG. Sai dai a wannan karon kocinsa Koeman ya sha alwashin yin dukkan kokari wajen gamsar da Messi kan cigaba da takawa Barcelona leda.

Karo na farko kenan dai da Messi ba zai haska zagayen kwata final na gasar Zakarun Turai ba sakamakon kayen da suka sha a hannun PSG, yanayin da rabon da Messi ya shiga tun kakar wasa ta 2004/2005 lokacin da Chelsea ta fitar dasu daga gasar Turan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.