Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester City ta nesanta kanta da zawarcin Messi

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta nesanta kanta dangane da alakanta kungiyar da zawarcin dan wasan gaban na Barcelona Lionel Messi.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi yayin fafatawarsu da PSG a Camp Nou
Dan wasan Barcelona Lionel Messi yayin fafatawarsu da PSG a Camp Nou REUTERS/Albert Gea
Talla

A karshen wannan kaka kwantiragi Dan wasan gaban na Argentina ke karewa tare da Barcelona.

Yiwuwar sake fitcewar Barcelona daga neman Kofin gasar Zakarun Turai ya kara ruruta tunanin cewa Messi na iya barin Nou Camp.

To sai dai har yanzu rashin tabbas yaci gaba da fitowa karara a kungiyar cikin yanayi na zaben sabon shugaban kungiyar, duk da cewa dukkannin 'yan takarar na cewa sun kuduri aniyar sabanta kwantiragin dan wasan mai shekaru 33.

Messi ya lashe Ballon D'Or har guda 6, kan rawar da ya taka sabgar tamola, wanda aka tabbatar da shi amatsayin daya daga cikin fitattun 'yan wasan duniya.

An daɗe ana rade-radin cewa City na bukatan Messi, saboda kusancinsa da tsohon kocinsa Pep Guardiola, kodayake Paris St-Germain ma ana ganin tana da sha'awar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.