Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi na shan caccaka kan kasa ceto Barcelona daga kamun kazar kukun PSG

Kaftin din Barcelona Lionel Messi na shan caccaka daga wasu magoya baya, da kuma masu sharhi kan tamaula, dangane da gazawar da wasu ke ganin yayi wajen taimakawa Barcelona yayin wasan da PSG ta lallasa su da 4-1 har gida Camp Nou a gasar Zakarun Turai.

Kaftin din Barcelona Lionel Messi tare da tauraron PSG Kylian Mbappe, yayin fafatawar su a gasar Zakarun Turai. 16/2/2021.
Kaftin din Barcelona Lionel Messi tare da tauraron PSG Kylian Mbappe, yayin fafatawar su a gasar Zakarun Turai. 16/2/2021. REUTERS
Talla

Tsohon dan wasan Chelsea Joe Cole ne na baya bayan nan da ya caccaki Messi, wanda yace alamu sun nuna cewa zuciyar kaftin din ba ta tare da kungiyar sa.

Joe Cole ya kuma gargadi kocin Manchester City Pep Guardiola da cewar, ya guji kulla yarjejeniya da Messi domin a cewarsa a halin yanzu kallon kitse ake yiwa rogo.

A kakar wasan da ta gabata dangantaka tayi tsami tsakanin Messi da Barcelona, bayan da suka sha mummunan kaye a wasan gasar Zakarun Turan da Bayern Munich ta lallasa su da 8-2 a zagayen kwata final.

A waccan lokacin dai Messi yayi yunkurin tilastawa Barcelona kyale shi ya sauya sheka kamar yadda yake kunshe cikin yarjejeniyarsa da kungiyar, wadda a karkashinta yake da zabin rabuwa da ita a karshen kakar wasa, ko da kuwa wa'adin yarjejeniyar bai kare ba.

A halin yanzu kungiyoyin da ake alakanta Messi da su sun hada da PSG da kuma Manchester City wadda a shekarar bara suka soma tuntubar juna.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.