Isa ga babban shafi
Wasanni

Munich ta lallasa Chelsea, Barcelona tayi kunnen doki da Napoli

Kungiyar Bayern Munich ta lallasa Chelsea da kwallaye 3-0 yayin fafatawarsu jiya talata a wasan farko na zagayen gasar zakarun Turai na 2 da ya kunshi kungiyoyi 16.

Dan wasan gaba na kungiyar Bayern Munich Robert Lewandowski yayin jefa kwallo ta 3 a ragar Chelsea yayin gasar Zakarun Turai.
Dan wasan gaba na kungiyar Bayern Munich Robert Lewandowski yayin jefa kwallo ta 3 a ragar Chelsea yayin gasar Zakarun Turai. REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Munich ta lallasa Chelsea har gida ne ta hannun ‘yan wasanta Serge Gnabry da ya ci kwallaye 2, yayinda Robert Lewondoski ya ci ta 3, kwallo kuma ta 11 da ya ci kenan a gasar cin kofin zakarun Turan ta bana.

Sai kuma ranar 18 ga watan Maris Chelsea za ta yi tattaki zuwa Jamus don fafatawa karo na 2.

Ita kuwa Barcelona kunnen 1-1 ta tashi bayan yin tattaki zuwa Italiya indata fafata da Napoli a gasar at Zakarun Turai.

Dan wasan Napoli Dries Mertens ya soma jefawa Barcelona kwallo, kafin daga bisani Antoine Griezmann ya rama musu.

Fafatawa ta 2 za ta gudana a gidan Barcelona ranar 18 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.