Isa ga babban shafi
Wasanni

Cheptegei ya kafa sabon tarihi a gasar gudun yada-kanin-wani

Joshua Cheptegei dan kasar Uganda ya kafa tarihin zama dan tsaren gudun yada-kanin-wani a duniya da ya shafe gudun kilomita 5 cikin mintuna 12 da dakika 51, yayin gasar tseren da birnin Monaco ke karbar bakunci a Faransa.

Zakaran tseren gudun yada-kanin wani na duniya, Joshua Cheptegei dan kasar Uganda.
Zakaran tseren gudun yada-kanin wani na duniya, Joshua Cheptegei dan kasar Uganda. REUTERS/Lucy Nicholson
Talla

Jimmy Gressier dan kasar Faransa ne ya zo na 2 a gasar tseren na yada-kanin-wani, bayan kammala gudun na kilomita 5 cikin mintuna 13 da dakika 18, abinda ya bashi damar zama mafi saurin kammala gasar yanzu haka a nahiyar Turai.

A shekarun bayan Rhonex Kipruto na kasar Kenya ne ke rike da kambin mafi saurin kammala tseren na kilomita 5 a duniya, bayan kammalawa cikin mintuna 13 da dakika 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.