Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Chelsea na daf da sayen dan wasan gaban Ajax

Tattaunawa ta yi nisa tsakanin Chelsea da Ajax kan sayen dan wasan gaba Hakim Ziyech a wannan kaka kan kudi fam miliyan 38, kuma nan ba da dadewa ba zaa sanar da kammaluwar cinikin.

Wasu 'yan wasan  Chelsea.
Wasu 'yan wasan Chelsea. REUTERS/Eddie Keogh
Talla

A watan Janairu Chelsea ta so sayen dan wasan mai shekaru 26, amma kungiyar Ajax ta nuna ba za ta sayar ba saboda kokarin da take na lashe gasar kasar Holland.

Sayen dan wasan dan kasar Morocco da Chelsea za ta yi, zai kasance na farko tun bayan haramcin da aka wa kungiyar na sayen sabbin ‘yan wasa.

An sha rade radin cewa Chelsea za ta sayi wasu ‘yan wasa a lokacin da aka bude kasuwar hada – hadar ‘yan wasa ta watan Janairu cikin su har da dan wasan gaba na Paris Saint Germain Edinson Cavani da na Napoli Dries Mertens.

Ziyech ya bada gudummawa a canjaras da aka yi a haduwa tsakanin Ajax da Chelsea 4-4 a watan Nuwamba a gasar zakarun nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.