Isa ga babban shafi
Wasanni

Magoya bayan Manchester United sun hasala da nasarar Burnley

Bayan shan kaye har gida da kwallaye 2 da banza a hannun Burnley, magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United sun rika tofin alatsine ga tawagar kungiyar wadda suka bayyana da mafi lalaci da Club din ya taba fuskanta a tarihi.

Manchester United bayan shan kayen bazata.
Manchester United bayan shan kayen bazata. Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Wannan dai ne karon farko da Burnley ta taba yin nasara kan United har gida a tarihin gasar Firimiya, matakin da ya harzuka magoya bayan na United wadanda basu kammala murmurewa daga shan kayen da suka yi hannun Liverpool a karshen mako ba.

Yayin wasan na jiya dai Chris Wood ne ya budewa Bunley nasara da kwallonta na farko kafin daga bisani bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Jay Rodriguez ya kara kwallo ta biyu ba tare da United ta farke ba.

Kafin nasarar ta jiya, shekara 3 kenan a jere United na lallasa Burnley a Old Trafford da kwallaye 2 da nema.

A wasan na jiya dai magoya bayan United sun rika ife-ife da wake-waken kushe tawagar baya ga nuna bacin ransu kan rashin nasarar, inda bayan dawowa daga hutun rabin lokaci abin ya tsananta yayinda mintuna 7 zuwa 5 kafin a karkare wasa dubun-dubatar magoya bayan na United suka rika ficewa daga fili don nuna bacin ransu ga wasan.

Manchester United wadda ta doka wasan na jiya ba tare da Marcus Rashford da ke jinya ba, yanzu haka ita ke matsayin ta 5 a teburin Firimiya kasa da Chelsea da tazarar maki 6, ko da dai Club din ya sha alwashin karkare gasar a jerin ‘yan hudun saman teburi.

A bangare guda nasarar ta jiya ta baiwa Burnley damar farfadowa zuwa matakin ta 13 a teburin na Firimiya da maki 30.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.