Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Pogba na son kawo karshen wariya a kwallon kafa

Dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba ya kaddamar da wata zanga-zangar mutum guda don kalubalantar nuna wariyar a wasannin kwallon kafa da ke kara ta’azzara a nahiyar Turai.

Paul Pogb dan wasan tsakiya na Manchester United.
Paul Pogb dan wasan tsakiya na Manchester United. Reuters
Talla

Pogba dan faransa mai shekaru 26 wanda ya kauracewa wasan jiya Alhamis da United ta lallasa Newcastle da kwallaye 4 da 1, an ganshi cikin ‘yan kallo sanye da wani awarwaro mai launin fari da baki a jikinsa an rubuta ‘‘ akawo karshen wariya, dukkanninmu daya ne’’

Ka zalika Pogba ya bukaci abokan wasanshi na United dukkanninsu su sanya irin awarwaron yayin wasan, inda a bangare guda kuma ya rarraba irinsa ga tarin magoya bayansa da suka halarci filin wasan.

Bayan kammala wasan na jiya dai Pogba ya kuma wallafa wani salon magana a shafinsa na Twitter inda ya aro kalaman Martin Luther da ke cewa Kiyayya baza ta taba magance kiyayya ba, sai dai soyayya ta yi, inda daga can kasa kuma dan wasan ya rubuta a kawo karshen nuna wariya dukkanninmu daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.