Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Liverpool na ci gaba da jan zarenta a Firimiyar Ingila

Liverpool ta jaddada jagorancin da take a kan teburin gasar Firimiyar Ingila bayan ta doke mai bi mata a teburin, Liecester City har gida a filin wasa na King Power, lamarin da ya sa yanzu ratar maki 13 ta ba Leicester.

'Yan wasan  Liverpool yayin murnar saka kwallo a raga.
'Yan wasan Liverpool yayin murnar saka kwallo a raga. Phil Noble/Reuters
Talla

Tawagar ta Jurgen Klopp ta shiga wasan na Alhamis ne da ratar maki 10 tsakaninta da Liecester, sannan kuma ta gwada bajintar da ta sa ake ganin babu abin da zai hana ta lashe wannan kofin karon farko cikin shekaru 30.

Roberto Firmino ne ya fara ci wa Liverpool kwallo a wasan, da taimakon Trent Alexander-Arnold kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Leicester na ganin zata farke wannan kwallo ne kawai sai dan wasanta Caglar Soyuncu ya taba kwallo da hannu a cikin da’ira ta 18 a minti na 71, shi ko dan wasan Liverpool da ya shigo bayan hutu, James Milner bai yi wata wata ba ya saka bugun daga – kai - sai - mai – tsaron - raga da alkalin wasa ya bayar cikin raga.

Daf da za a tashi wasa ne kuma har ila yau da taimakon Alexander-Arnold, Firmino, ya sake cin wata kwallon, bayan haka ne kuma Alexander Arnold ya saka tashi a raga, wasa ya zama Liverpool 4 Leicester 0.

A halin da ake ciki, maki biyu ne kawai Liverpool ta rasa daga wasanni 18 da ta buga, yanzu manazarta harkar kwallon kafa na ganin zai yi matukar wahala wata kungiya ta yi mata juyin mulki cikin sauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.