Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Arsenal ta dawo turba bayan lallasa West Ham da kwallaye 3 da 1

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kawo karshen rashin nasarar da ta yi fama dashi a tsawon wasanni 9 bayanda a daren jiya Litinin ta lallasa West Ham United har gida da kwallaye 3 da 1 nasarar da ke matsayin ta farko ga sabon kocin rikon kwaryar Club din Freddie Ljunberg.

Dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang.
Dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang. REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Har dai aka tafi hutun rabin lokaci West Ham ce ke jagoranci bayan kwallonta daya tilo da ta zura a minti na 38 da fara wasa ta hannun dan wasanta Angelo Ogbonna.

Amma kuma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne labari ya sauya inda Gabriel Martinelli matashin dan wasan Arsenal da wannan ne karon farko da ya yi cikakken wasa na mintuna 90 ya zurawa Arsenal kwallonta ta farko a minti na 60, kana Nicolas Pepe ya kara ta biyun a minti na 66 tukuna Aubameyang ya zura kwallonta 3 a minti na 69, wato dai cikin wa’adin da bai wuce mintuna 10 ba ne Arsenal ta yiwa West Ham ruwan kwallayen har 3.

Yanzu dai Arsenal da matsa gaba da mataki biyu a teburin Firimiya inda ta ke matsayin ta 9 da maki 22.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.